Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ya yi watsi da sabon ikirari da hadaddiyar daular larabawa ta yi kan tsibiran iran guda 3, kuma ta yi tir da matakin da Abu dhabi ta dauka na yin amfani da ganawar diplomasiya wajen tabbatar da ikirarinta mara tushe.
Wannan hatsaniyar kai tsaye ta shafi dukkan kasar Iran ne, kuma ta kafa tarihi mai muhimmanci a tsakanin ci gaban diflomasiyar yankin da manyan kasashe kamar china ke fuskanta, don haka Tehran na daukar maimaita irin wannan ikirarin a matsayin kerya dokokin kasa da kasa da kuma kyakkyawar alakar makwabtaka.
Kakakin ma”aikatar harkokin wajen iran isma’ila Bagha’I ya nuna takaicinsa game da dagewar da hadaddiyar daular larabawa tayi na yin amfani da kasancewar jama’ain diflomasiya wajen tado da ikirarinta kan kasar iran.
Haka zalika yayi tir da maimaita irin wannan ikirari da ba shi da tushe kuma kuskure ne , game da tsibiran kasar iran wato Abu musa , tumbu babba da tunbu karami a bayanan karshe da tayi a lokacin ziyarar ministan harkokin wajen china a Abu dhabi