Lavrov: Kasashen Yamma sun mayar da Hukumar IAEA dandalin siyasa

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov, a wata hira da gdan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) a ranar 15 ga Disamba, ya yi

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov, a wata hira da gdan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) a ranar 15 ga Disamba, ya yi magana kan wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa, ciki har da shirin nukiliyar farar hula na Iran, yakin Ukraine, da raguwar tasirin kasashen Yamma a duniya.

Da yake magana tun da farko game da rikicin da ke tattare da shirin nukiliya na Iran, ya ce Amurka ta janye kanta daga shirin hadin gwiwa na (JCPOA) a shekarar 2018, wanda hakan ya wargaza yarjejeniyar da kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.

Lavrov ya jaddada cewa Iran ta cika dukkan sharuddan yarjejeniyar har sai da Washington ta bayyana janyewarta daga yarjejeniyar, matakin da ya bayyana a matsayin keta dukkan dokoki da ka’idoji na kasa da kasa. Ya ce kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231, wanda ya ginu kan yarjejeniyar, wanda kuma Amurka ta jefa shi cikin kwandon shara, inji Lavrov.

Ya kara da cewa gwamnatocin Yamma daga baya sun yi kokarin mayar da laifin a kan Iran,  duk da cewa Iran ta bi yarjejeniyar da aka rubuta sau da kafa. Ya ce wannan ya nuna wani sauyi a cikin rushewar amincin diflomasiyyar duniya.

“Ina ganin abin kunya ne ga diflomasiyyar duniya lokacin da suka matsa lamba kan shawarar sake sanya takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da wani salo na yaudara, wanda a cewarsa Jami’an diflomasiyya na gaskiya da gaskiya ba sa yin haka.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted