Wata kotu a Faransa ta yanke wa wani tsohon jagoran yan tawaye a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, Roger Lumbala hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samun sa da hannu a laifin cin zarafin ɗan adam a yayin yaƙin Congo na biyu, hukuncin da ƴan gwagwarmaya suka bayyana a matsayin mai matuƙar mahimmanci.
An tuhumi Lumbala ne da kasancewa ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa ta’asa da aka yi a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo daga shekarar 2002 zuwa 2003, kuma tun a wata daya gabata aka gurfanar da shhi a gaban ƙuliya, bayan da aka kama shi a Faransa a shekarar 2020.
Tsohon ɗan tawayen, wanda ya musanta aikata ba daidai ba, ya ƙi halartar zama kotun tun da aka fara shari’ar, ya kasance a kotun domin sauraron hukuncin.
Amma hukuncin na wannan Litinin, shine irin sa na farko da wata kotun ƙasa, a ƙarƙashin ƙudirin da ta bai wa kotunan cikin gida damar hukunta waɗanda suka aikata manyaan laifuka kamar kisan ƙare dangi da sauransu, kamar yadda ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka bayyana.