Iran: Wani Mai Takardun Kasa Biyu Yana Fuskantar Sharia Saboda Leken Asiri Wa HKI A Yakin Kwanaki 12

Kakakin ma’aikatar Sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa a halin yanzun wani mai yan kasanci biyu a kasar yana fuskantar sharia saboda aikin

Kakakin ma’aikatar Sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa a halin yanzun wani mai yan kasanci biyu a kasar yana fuskantar sharia saboda aikin leken asiriwa wa HKI a yakin kwanaki 12 wanda Amirka da HKI suka dorawa kasar a cikin watan Yunin da ya gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Asghar Jahangir yana fadar haka a lokacinda yake jawabi gay an jaridu a nan Tehran a yau Talata. Ya kuma kara da cewa.

Ya kara da cewa mutumin wanda aka kama shi a garin Karaj na lardin Albus dake kusa da nan Tehran, ya fara aiki da hukumar leken asiri ta HKI MOSAD ne a shekara ta 2023.

Kuma ya sami zama dan kasar Sweezland a shekara ta 2020, sannan daga baya ya ziyarci kasashen turai har guda 6 inda ya sami horaswa ta ayyukan leken asiri. Sannan ya je HKI ya kuma dawo kasar Iran wata guda kafin yakin kwanaki 12.

A lokacinda dakarun IRGC suka kama shi yana zaune ne a wani kataparen gidansa da ke wajen birnin Karaj a nan kusa da birninTehran. Kuma ya aikewa HKI asiran JMI da dama. Ana saran nan ba da dadewa ba wata kotu a karaj zata yanke masa hukuncin da ya dace da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted