Iran Ta Bukaci Abi Sahihiyar Hanya Wajen Zaben Sabon Sakatare Janar Din M D D

Rahotanni sun bayyana cewa iran tayi kira da abi sahihiyar hanya wajen zaben sabon sakatare janar din majalisar dinkin duniya , tayi gargadin cewa duk

Rahotanni sun bayyana cewa iran tayi kira da abi sahihiyar hanya wajen zaben sabon sakatare janar din majalisar dinkin duniya , tayi gargadin cewa duk wanda yayi gum da bakinsa kan harin da akai wa cibiyoyin nukiliyar iran hari to bai cancanta ba, a wani jurwaye mai kamar wanka ga shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi

A cikin jawabin da yayi a lokacin zaman kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya litinin  jakadan dindindin na kasar iran a kwamitin  Amir sa’id iravani ya bayyana mahangar iran kan kaidoji masu tasiri kan zaben sabon shugaban majalisar dinkin duniya .

Ya bayyana cewa karfin da kuduri mai lamba 99 ya bayar zai ba dama ga sakataren janar ya gabatar da barazanar da zaman lafiyar duniya ke fuskanta ga kwamitin tsaro, amma bai kai ga nasara ba sakamakon hawa kujerar naki da daya daga cikin masu kujerar dindindin a majalisar yayi,

Jakadan yana ishara ne ga harin da Amurka da isra’ila suka kai a watan yuli kan cibiyar nukiliyar iran na zaman lafiya dake karkashin kulawar hukumar nukiliya ta duniya, yace wannan mataki na karya doka  ya shafi masana kimiyar kasar, wanda shugaban hukumar nukiliyar ke jagoranta , amma yanzu ya sanar da kasancewa dan takarar neman kujerar majalisar dinkin duniya da ya kasa yin tir da kai harin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted