Majiyar dakarun juyin juya halin musulunci na kasar Iran ta bada sanarwan cewa makaman HKI sun sami nasarar lalata kasha 3% ne kacal na damdamalin cilla makamai masu linzami na kasar Iran a yakin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen na kasar Lenanon ta nakalto majiyar dakarun juyin juya halin musulunci na kasar Iran na fadar haka a yau Talata. Majiyar ta kara da cewa zancen da jami’an gwamnatin HKI suke yadawa kan cewa sun lalata mafi yawan wuraren cilla makamai masu linzami na kasar ba gaskiya bane.
Majiyar ta kara da cewa, rundunar sojojin IRGC a shirye suke su cilla makamai masu linzami masu karfi a kan HKI a duk lokacinda suka sake kuskuren kaiwa kasar Hari.
Majiyar ta kasar da cewa mafi yawan sansanonin cilla makamai masu linzami na dakarun IRGC, HKI ba za iya kai masu hare-hare ba, ballantana ta lalatasu.
Daga karshe bayanin ya kara da cewa, karfin makamai masu linzami na JMI yana nan daram sai kuma kara karfi suke, don nika duk wanda yayi gigin kaiwa kasar hari.