Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf, ya bayyana cewa magance matsalolin da kasar Iran ta ke fuskanta a bangarori da dama zasu warwaru ne ta hanyar masana masu bincike a fannonin ilmi daban-daban.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka ne a lokacinda yake jawabi a gaban zababbun masu bincike a kasar wadanda suka ziyarci majalisar dokokin kasar a dai-dai makon masu bincike a nan kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa, kakakin majalisar dokokin kasar ya gana da masu binciken a dakin taro na Shahid Sheikh Fazlollah Nouri ya kuma taya masu binciken murnan zagayowar makon bincike na kasa. Ya kuma bayyana muhimmancin bincike da kuma masu binciken ilmi a kasar wajen warware matsalolin kasar a shekarun da suka gabata, kuma yana ganin manya-manyan matsalolin da ake fama da su a kasa wadanda suke bukatar bincike ba zai fi karfin masu bincike na kasar ba.
Yace hatta tafiyar da gwamnati tana bukatar bincike da kuma gabatar da al-amura bisa ilmi wanda bincike ya tabbatar da shi. Kuma hakan zai baya shuwagabanni daukar shawarorin da suka dace a ko wani lokaci.
Daga karshe yace majalisar dokokin kasar tana bukatar taimakon masu bincike, kamar yadda kuma a shirye teke ta taimaka masu a duk idan bukatar taimako ta tashi a cikin ayyukansu na bincike.