Grossi: Rasha za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen warware batun nukiliyar Iran

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya bayyana cewa Rasha za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa wajen warware batun nukiliyar

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya bayyana cewa Rasha za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa wajen warware batun nukiliyar Iran.

Rafael Grossi ya yi wannan tsokaci ne ga kamfanin dilancin labaran Rasha na Sputnik inda ya bayyana cewa gwamnatin Moscow za ta iya taka mahimmiyar rawa wajen samar da mafita ga shirin nukiliyar Iran.

Ya ce kan wannan batun ya samu damar tattaunawa da Vladimir Putin, Shugaban Rasha, da kuma Ministan Harkokin Wajen kasar, da kuma Darakta Janar na Rosatom, da kuma jami’an Ma’aikatar Tsaron Rasha.”

Alaka tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ta shiga rashin tabbas tun bayan hare-haren hadin guiwa na Amurka da Isra’ila akan cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yuni da ya gabata.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted