Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI

Hukumomin Mali sun dakatar da watsa shirye-shiryen tashoshin gidajen talabijin na kasar Faransa TF1 da LCI a fadin kasar. Hukumar Sadarwa ta Mali ta bayar

Hukumomin Mali sun dakatar da watsa shirye-shiryen tashoshin gidajen talabijin na kasar Faransa TF1 da LCI a fadin kasar.

Hukumar Sadarwa ta Mali ta bayar da dalilan dakatar da wadanan tashohin bisa wani shiri da tashar LCI ta yi kan halin da ake ciki sakamakon matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi.

Shirin mai suna “Grands Dossiers” da aka watsa a LCI a ranar Lahadi, 9 ga Nuwamba, wanda aka raba zuwa sassa biyu ya kunshi kanun labarai kamar haka ” Masu ikirarin Jihadi a Kofofin Bamako” da kuma “Mali, Karkashin kungiyar Al-Qaeda.”

A sashen guda, wanda aka dora a shafin yanar gizon tashar TF1+, rahoton yi ikirarin cewa gwamnatin mulkin soja ta haramta sayar da mai, kuma yankunan  Kayes da Nioro suna killace, kuma ‘yan ta’adda suna kusa da kwace babban birnin.

A cewar hukumomin Mali, hakan ya karya ka’idar da’a ga ‘yan jarida a Mali, wanda ke bukatar su yi gaskiya da kuma buga bayanai da aka tabbatar.

Takun tsaka tsakanin Mali da Faransa ya yi kamari tun bayan da sojoji suka kwace mulki a kasar.

Kuma wannan ba shi ne karon farko da Mali ke dakatar da watsa shirye shiryen gidajen talabajin da radiyo na faransa a kasar ba.

A cen baya Mali ta dakatar da watsa shirye shiryen gidan radiyo RFI da kuma tashar talabijin ta France24 a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments