Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha mariya zakhrova ta bayyana cewa Mosko ba ta da wani shirin na kai hari kan wata mamba a kungiyar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha mariya zakhrova ta bayyana cewa Mosko ba ta da wani shirin na kai hari kan wata mamba a kungiyar tsaro ta Nato amma ta shirya mayar da martani kan duk wanda ya kai mata hari daga mambobin kungiyar.

Da take taron manenma labarai mariya ta zayyana cewa tana kara  maimaitawa  babu wani shiri na kai hari kan wata kasa dake mamba a kungiyar tsaro ta nato , sai dai kasar rasha ta riga ta dauki mataken da suka dace na ganin ta samar da tsaronta, adaidai lokacin da abokan hamayya suke gina sansanin soja kusa da iyakar kasarta

A cewa Jami’in diplomasiya, bayanan da wasu jami’an kungiyar tsaro ta nato suka fitar bangare ne na wani shiri ne da aka tsare don samar da daidaito tsakanin alumma da haifar da farga da kuma sanyawa mutane su amince da raayin dake nuna cewa babu makawa rikici tsakaninta da Kasar Rasha.

Ko a watan jiya ma ministan harkokin wajen kasar rasha Sargie Lavrov ya fadi a watan jiya cewa Mosko a shirye take ta bada tabbacin rashin shirin kaiwa Nato ko kasashen turai wani hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted