M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan

Babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterre yayi kakkausar suka game da harin da yahudawa yan share wuri zauna suka kai kan wani

Babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterre yayi kakkausar suka game da harin da yahudawa yan share wuri zauna suka kai kan wani masallaci da ya kai ga konewa a Dair Istiya dake yankin da isra’ila ta mamaye a gabar yamamcin kogin jodan,

 Matakin na majalsiar dinkin duniya na yi tir da kai harin ya nuna irin yadda duniya ta damu matuka game da fitinar da yahudawa yan share wuri zauna suke tayarwa da rawar da suke takawa wajen karuwa rashin zaman lafiya, tsaro a yankunan da aka mamaye.

Hare-hare da sojojin isra’ila da yahudawan yan share wuri zaune ke kai wa ya karu sosai a gabar yammacin kogin jodan tun bayan harin oktoba 2023 inda akalla falasdinawa1070 suka rasa rayukansu wani adadi mai yawa kuma suka jikkata,

A wantan yuli kotun duniya mai hukumta manyan laifu sun sanar da ci gaba da mamaye yankunan falasdina wanda yin gine-gine ya sabama doka, kuma tayi kira da ta fice daga dukkan yankunan da ta mamaye a gabar yammacin kogin jodan da kuma gabashin Qudus.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted