Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin Trump

Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da shirin zaman lafiya na shugaba Donald Trump. Amurkar da wasu abokan

Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da shirin zaman lafiya na shugaba Donald Trump.

Amurkar da wasu abokan huldarta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin Amurka wanda ya amince da shirin zaman lafiya na Donald Trump kan Gaza, yayin da Rasha ta gabatar da wani daftarin kuduri na daban kan Gaza.

“Amurka, Qatar, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Indonesia, Pakistan, Jordan, da Turkiyya sun bayyana goyon bayansu ga daftarin kudurin na Amurka wanda ya tanadi kafa kwamiti da zai kula da gwamnatin rikon kwarya a Gaza da rundunar kasa da kasa a yankin Falasdinu, da kuma fatan amincewa da shi cikin sauri,” in ji su a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.

A ranar Alhamis, Amurka ta yi gargadi game da hadarin rashin amincewa da daftarin kudurin, Yayin da kasashen Larabawa ke nuna fargabar darewar yankin gida biyu.

Rasha ta rarraba wani daftarin kuduri kan Gaza ga membobin Kwamitin Tsaro na MDD, mai kalubalantar na Amurka, wanda ke bukatar MDD ta samar da hanyoyin karfafa shirin na zaman lafiya amma ba tare da ambatar shirin na shugaban Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments