Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000

Jamhuiryar Demokradiyyar Congo ta fitar da  ma’adanin ‘Colbat’ da ya kai ton 1,000 a karon farko. Shi  dai wannan ma’adanin ne ake amfani da shi

Jamhuiryar Demokradiyyar Congo ta fitar da  ma’adanin ‘Colbat’ da ya kai ton 1,000 a karon farko.

Shi  dai wannan ma’adanin ne ake amfani da shi wajen yin batirin “Lithium-ion” masu cajin motoci mai amfani da wutar lantarki, wayoyin hannu, kwamfuta da suaransu. Bugu da kari wannan ma’adanin yana taka rawa wajen kauracewa amfani da makamashin da da yake gurbata muhalli.

A cikin kasar DRC kadai ne ake samun kaso 72 % na dukkanin wannan ma’adanin da ake da shi a duniya. Da akwai mutanen da sun kai miliyan 1.5 da suke aiki a wuraren hako wannan ma’adanin a cikin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments