Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD ta ce; Da akwai fiye da mutane 100,000 da su ka fice daga birnin Al-Fasher makwanni biyu kadai bayan da da kungiyar RSF ta shimfida ikonta a cikinsa.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan hijirar ta MDD, ta kuma ce abu ne mai yiyuwa a halin yanzu adadin wadanda su k fice daga cikinbirnin sun fi haka,domin da akwai wadanda su ka makale akan hanya suna ci gaba da tafiya, wasu kuma suna cikin birnin suna son ficewa.
Mutanen da suke ficewa suna son isa yankunan da suke da nisa sosai kamar kilo mita 50 daga gundumar Darfur. Wasu kuma suna tafiyar dubban kilo mita daga yankin baki daya.
Sai dai kuma hukumar ‘yan hijirar ta ce,nisan da masu ficewa daga Al-Fasher suke yi, yana kara jefa su cikin hatsari saboda rashin abinci da ruwan sha aka hanya.
A yayin kutsen da rundunar RSF ta yi a cikin birnin na Al-Fasher ta aikata laifukan yaki da su ka hada kisan kiyashi, cin zarafi da wawason dukiyar mutanen birnin.
Hukumar yan hijirar ta MDD ta kuma ce, a fadin kasar Sudan da akwai mutanen da sun kai miliyan 30 da suke da bukatuwa da agaji na gaggawa.
A jiya Juma’a ne dai hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta amince da kafa kwamitin da zai bincika laifukan da aka yi a Darfur,musamma a birnin Al-Fasher.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne dai mayakan rundunar kai daukin gaggawa ta RSF su ka kutsa cikin birnin na Al-Fsher, da shi ne cibiyar mulkin ta Darfur ta,, tare da cin zarafin mutanen dake ciki, bayan killace su na watanni 18.