Dakin Gwaje-gwaje na “Sandia” dake karkashin ma’aikatar makamashin Amurka ya sanar da cewa; Jirgin sama samfurin “F-35” ya jefa bom din Nukiliya ba tare da yana dauke da abubuwan da suke fashewa a ciki ba.
Majiyar ta kara da cewa an yi wannan gwajin ne dai a yankin Nivada na kasar ta Amurka a tsakanin 19 zuwa 21 ga watan Ogusta a karkashin sake duba lafiyar makamin Nukiliyar kasa da kuma kara bai wa matuka jiragen saman yaki horo.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada niyyarsa ta ganin Amurka ta koma kan yin gwaje-gwajen makaman Nukiliya ba da jimawa ba. Sai dai shugaban na Amurka bai bayar da wani Karin bayani akan haka ba.
Sai dai kuma wani labarin yana cewa ba da jimawa ba, jami’an ma’aikatar makamashin Amurka za su gana da shugaba Donald Trump a fadar mulkin kasar ta “White House” domin nuna masa kin amincewarsu da yin amfani da makaman Nukiliyar na gaske a wajen gwaji.” Tashar talabijin din CNN ce ta dauko wannan labarin.