Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur

Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje […]
Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake […]
Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka

Shugaban tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya […]
Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita

Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu […]
Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar

‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista […]
Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar

Ministan Harkokin Wajen Sudan Mohieldin Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da cin zarafin dan Adam da Rundunar Taimakon Gaggawa ta (RSF) ke yi a yankunan El-Fasher, Darfur ta Arewa, da Bara, da Kordofan ta Arewa. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin wani taro […]
Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi a karatu na farko da wani kudiri da aka gabatar mata na yin hukunci kisa kan wadanda aka kama da laifin ta’addanci a kasar. Dan majalisar kasar mai tsattsauran ra’ayi, Itama Ben Gvir ne ya gabatar da kudirin, […]
Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya

Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron […]
Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10

A kasar Lebanon an sanar da sakin dan tsohon shugaban kasar Libya, Hannibal bisa kudin fansa da sun kai dala 900,000. An tsare dan gidan Kaddafi din ne bisa tuhumarsa da boye bayanai masu alaka da bacewar Sayyid Musa As-Sadr da abokan tafiyarsa, wanda tsohon shugaban kasar ta Libya yake da hannu. Majiyar tsaro da […]
An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali

A Jiya Litinin an sake bude gidajen sayar da man fetur da aka rufe a cikin birnin Bamako saboda killace iyakokin kasar a kungiyar masu dauke da makamai mai alaka da alka’ida ta yi ta hana shigar da makamashi. Har ila yau an bude wasu makarantun a cikin birnin na Bamako da safiyar jiya Litinin,kamar […]
Trump Ya Yi Wa Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama Barazana

Shugaban kasar Amurka ya yi wa ma’aikatan filayen jiragen sama masu sa idanu akan sauka da tashin jirage, barazana. Ma’aikatan da suke sanya idanu a cikin hasumiyoyin dake filayen jiragen sama da dama ne a Najeriya su ka dakatar da ayyukansu saboda rufe ayyukan gwamnati da aka yi a kasar, domin ba za su sami […]
Donald Trump Na Amurka Ya Karbi Bakuncin Shugaban Rikon Kwaryar Kasar Syria Ahmad Shar

Ganawa a tsakanin bangarorin biyu dai ta mayar da hankali ne akan batutuwan da su ka shafi dauke wa Syria takunkumi, shigar da kungiyar Kurdawa a cikin sojojin kasar, da kuma alaka a tsakanin Damascuss da Haramtacciyar Kasar Isra’ila. A nashi gefen ministan harkokin wajen Syria As’ad Shaibani ya bayyana ganawar da cewa ta yi […]
Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da […]