Shugaban kasar Amurka ya yi wa ma’aikatan filayen jiragen sama masu sa idanu akan sauka da tashin jirage, barazana.
Ma’aikatan da suke sanya idanu a cikin hasumiyoyin dake filayen jiragen sama da dama ne a Najeriya su ka dakatar da ayyukansu saboda rufe ayyukan gwamnati da aka yi a kasar, domin ba za su sami albashi ba.
Shugaba Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta “Truth Social” cewa:, Ba ni jin dadin mutanen da ba su yin wani aiki sai korafi,alhali suna sane da cewa za a basu dukkanin hakkokinsu.”
Trump ya kuma yi wa ma’aikatan da ba su dakatar da ayyukansu ba alkawalin ba su kyautar kudi Dala 10,000 kowanensu.
Rufe ayyukan gwamnatin kasar ta Amurka wanda ake bayyanawa a matsayin mafi tsawo a tarihi ya sanya ma’aikatu da dama sun rage yawan ma’aikatansu daga ciki har da filayen saukar jiragen sama. Ana sa ran cewa idan har aka kai ranar Juma’a ba a kawo karshen rufe ayyukan gwamnatin ba,to yawan filayen jiragen saman da za a rufe za su kai 40%,da a halin yanzu suna a matssayin 10% ne.
Kamfanoni da dama na jiragen sama a Amurkan sun dakatar da zirga-zirgar matafiya.