Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10

A kasar Lebanon an sanar da sakin dan tsohon shugaban kasar Libya, Hannibal bisa kudin fansa da sun kai dala 900,000. An tsare dan gidan

A kasar Lebanon an sanar da sakin dan tsohon shugaban kasar Libya, Hannibal bisa kudin fansa da sun kai dala 900,000.

An tsare dan gidan Kaddafi din ne bisa tuhumarsa da boye bayanai masu alaka da bacewar Sayyid Musa As-Sadr da abokan tafiyarsa, wanda tsohon shugaban kasar ta Libya yake da hannu.

Majiyar tsaro da kuma ta shari’a a kasar Lebanon ta bayyana cewa; An saki Hannibal ne bayan da aka kammala dukkanin matakan sharia,sannan aka bai wa gidan kurkukun da ake tsare da shi, umarnin su bude kofa ya fita.

Tun a ranar 17 ga watan Oktoba ne dai wata kotu ta amince da a sake shi, bisa cewa zai bayar da dala miliyan 11, sai dai kuma daga baya an rage wannan kudin zuwa dala 893,000 saboda nuna rashin amincewar lauya mai ba shi kariya.

A 1978 ne dai Sayyid Musa As-Sadr da abokan tafiyarsa biyu, Muhammad Yakubi, da Abbas Badruddin su ka bace bayan da su ka isa cikin kasar Libya bisa gayyatar Mu’ammar Kaddafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments