Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita

Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Hayayi ya turnike sararin samaniyar Gaza

Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita.

Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai.

Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar da kuma kasashen da ke da alhakin aiwatar da ita.”

Tun bayan soma yakin Gaza a watan Oktonan 2023 jimillar wadanda sukayi shahada a Gaza ya kai 69,179, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 170,693, a cewar sabbin alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted