An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali

A Jiya Litinin an sake bude  gidajen sayar da man fetur  da aka rufe a cikin birnin Bamako saboda killace iyakokin kasar a kungiyar  masu

A Jiya Litinin an sake bude  gidajen sayar da man fetur  da aka rufe a cikin birnin Bamako saboda killace iyakokin kasar a kungiyar  masu dauke da makamai mai alaka da alka’ida ta yi ta hana shigar da makamashi.

Har ila yau an bude wasu makarantun a cikin birnin na Bamako da safiyar jiya Litinin,kamar kamfanin dillancin labarun “AP” ya nakalto.

Fiye da tankokin jigilar man fetur 100 ne masu dauke da makaman su ka kone kurmus, tare da kashe mutane da kuma kama matukansu da yin garkuwa da su.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kungiyar tarayyar Afirka ta fitar da bayani na yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki matakin fuskantar masu wuce gona da iri a Mali.

Haka nan kuma sanarwar ta yi tir da garkuwa da Misrawa uku da aka yi.

Masu bin diddigin abinda yake faruwa a Mali suna ganin cewa da akwai makarmashiyar abokan gaba a cikin lamarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments