Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake yi na cimma matsaya ta siyasa.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Masar, Tamim Khallaf, ya bayyana cewa Minista Abdel-Aty ya tabbatar a lokacin taron cewa matsayin Masar kan rikicin Libya, ya dogara ne kan bin tsarin siyasa da Libya take a kai ba tare da wani umarni ko tsangwama daga waje ba, a matsayin hanya daya tilo ta dawo da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.

Abdel-Aati ya sake nanata cikakken goyon bayan Masar ga kokarin Wakilin Musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na aiwatar da taswirar  Majalisar, yana mai jaddada muhimmancin “ci gaba da aiwatar da ginshiƙanta, wanda ya fi muhimmanci a cikinsu shi ne kafa sabuwar gwamnatin kan kasa wadda za ta shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa a lokaci guda,  yayin da yake jaddada buƙatar bin ƙa’idar da aka sanar domin kiyaye sahihancin tsarin siyasa da kuma cimma burin al’ummar Libya na samun kwanciyar hankali da ci gaba.”

Ministan Harkokin Waje ya kuma jaddada muhimmancin janye dukkan sojojin kasashen waje, mayakan kasashen waje da sojojin haya daga yankin Libya ba tare da wani sharaɗi ko jinkiri ba, bisa ga kudurorin kwamitin Tsaro, yana mai la’akari da wannan a matsayin muhimmin sharaɗi don cimma daidaito mai ɗorewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments