Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya

Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu

Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa.

Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin  jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam , kuma ya bayyana cewa an shirya harba tauraron dan adam guda uku na:  Zafar, Paya, da Kowsar  a farkon hunturu.

A cewar Pars Today, ya yi Ishara da hadin gwiwar da Iran ke yi da wasu kasashe a fannin sararin samaniya, yana mai ambaton ayyukan hadin gwiwar da China kan ayyukan  hadin gwiwar bincike da kasashen mambobin ECO. Wannan ayyukan hadin gwiwar sun hada da bada horo, haɓaka ayyukan bincike, da ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam.

Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya kuma yi magana kan sansanonin sararin samaniya na kasar, yana mai cewa sansanonin sararin samaniya na Almas da Konaran suna cikin matakan karshe kuma za a fara ayyukan a wadannan wurare nan ba da jimawa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted