Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa.
“Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi.
Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil.
Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma masu rajin kare muhallin na Ogoni su 9 sun cancanci a wanke su ta fukar shari’a.
Sunusi ya ci gaba da cewa, kisan da aka yi Ken Saro Wiwa da sauran abokan fafutukar tashi, na dabbanci ne, kuma an yi shi ne bisa zalunci, domin ba su aikata wani laifi ba,don haka iyalansu suna bukatar a yi musu adalci.
Sojoji sun kutsa cikin kauyuka 43 a yankin Ogoni tare da kashe mutane da dama a cikin watan Maris na 1994, sun kuma yi hakan ne bisa bukatar kamfanin na Shell.
An zartar da hukuncin kisa ne akan Ken Saro Wiwa da sauran abokan fafutukarsa 9 a ranar 10 ga watan Nuwamba na 1995