Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa

A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da […]
Pezeshkian: Hadin kan Musulmi zai iya dakile zalincin kasashen waje

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce hadin kai tsakanin kasashen Musulmi yana da matukar muhimmanci wajen kare muradunsu da tsaronsu, daga duk wani cin zarafi daga kasashen waje. Mista Pezeshkian ya yi wannan furuci ne a wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Oman Sayyid Hamoud bin Faisal al-Busaidi a Tehran yau Litinin. […]
Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila

Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka. A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta […]
Kashi 84% na ‘yan Faransa ba su gamsu da Macron ba a matsayin Shugaba

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da […]
Iran ta bukaci MDD ta nisanci nuna bangaranci game da masu keta dokokin duniya

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya […]
Kamaru : Paul Biya, ya lashe zaben shugaban kasar a karo na takwas

Majalisar tsarin mulki a jamhuriyar Kamaru ta sanar da Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wata. Mista Biya ya lashe zaben da kashi 53.66% na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar shugabancin kasar a wa’adin mulki na […]
An Nada Birgediya Janar Qarshi A Matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci

An naɗa Birgediya Janar Qarshi a matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Pakpour, ya fitar da wata doka da ta nada Birgediya Janar Seyyed Hujjatullah Ghoraishi a matsayin mataimakinsa na harkokin daidaitawa. Birgediya Janar Ghoraishi ya taba yin aiki a matsayin […]
Hamas Ta Ce: Kungiyar Ta Ba Da ‘Yanci Ga Masu Shiga Tsakani Zabar Membobin Kwamitin Gudanar Da Gaza

Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza Khalil al-Hayya, shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: ƙungiyar ta Hamas ta bai wa masu shiga tsakani ‘yancin zaɓar membobin kwamitin da za su gudanar da mulkin Gaza, wanda […]
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe ‘Yan kasar Lebanon Biyu Tare Da Jikkatan Wasu Biyu Na Daban

Mutane biyu ne suka yi shahada, yayin da wasu biyu suka jikkata a harin da Sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gabashin kasar Lebanon Hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata mota a garin Hafir yammacin Ba’alabak sun yi sanadiyyar shahadan mutane biyu tare da jikkata wasu biyu na […]
Amnesty International Ta Bukaci Bayyana Makomar Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil’Adama Da Suka Bace A Uganda

Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta matsa wa Uganda lamba ta bayyana makomar masu fafutukar kare hakkin bil’adama na Kenya Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International Kenya ta ƙara matsin lamba ga hukumomin Uganda kan su saki masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam na Kenya Bob Njagi da Nicholas Oyo, waɗanda suka […]
Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Yi Da’awar Kwace Karin Wasu Garuruwa A Sudan

Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa a Sudan ta karɓe iko da Barbi da El Fasher a daidai lokacin da ake gargaɗin jin kai Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta sanar da gwace iko da birnin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, jim kaɗan bayan sanar […]
Qalibaf: Sakon Iran, Rasha da China ga MDD manuniya ce ta hadin gwiwa mai karfi

Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi […]
Sheikh Naim: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke

Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke. Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, […]
Catherine Connolly ta lashe zaben shugaban Ireland

An zabi Catherine Connolly a matsayin shugabar Ireland a wani gagarumin sauyi na siyasa a Ireland, wanda hakan ke a matsayin wani lokaci na tarihi ga siyasar neman sauyi a Ireland. Connolly, ‘yar majalisa mai shekaru 68 daga Galway, ta lashe sama da kashi 64% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban Ireland, wanda […]
Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza

Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai illa ‘yancinsu na samun cin gashin kai a duniya. Khalil Al-Haya, shugaban Hamas a Gaza, ya fadi a wata hira da aka watsa ranar Lahadi cewa bangaren Falasdinawa yana da […]
Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher

Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar birnin El Fasher a hannun Dakarun RSF, tare da bayyan hakan a matsayin farganda da kuma yakin kwakwalwa. Sanarwar ta ce, “A halin yanzu ana fuskantar wani kamfen na kafofin […]