Sheikh Naim: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke

Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da

Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke.

Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, tabbas  za su fuskanci Isra’ilawa da dukkanin karfinsu, kuma ba za su bar Isra’ila ta mamaye kudancin Lebanon ba,ko da kuwa hakan zai kai ga shahadarsu ne baki daya.

Ya yi ishara da irin ayyukan wuce gona da iri da isr’ila ke yi akullum rana ta allaha  kan kasar Lebanon a kan idanun duniya, wanda hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar dakatar dayaki da aka cimmawa tare da ita, a maimakon masu shiga su taka mata burki, har kullum Amurka kara matsa lambta take yi kan kasar Lebanon domin amincewa da sharuddan Isra’ila.

Bugu da ƙari, ya yi gargaɗin cewa “idan maƙiya suka ƙaddamar da yaƙi a Lebanon, ba za su  cimma komai ba,” yana mai kira da a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa “kowa zai amfana idan aka tabbatar da yarjejeniyar.

Sakataren Janar na Hizbullah ya bayyana cewa Hizbullah ba za ta iya hana barkewar yaki ba, amma kuma za ta hana makiya cimma burinsu a kan kasar Lebanon.

Dangane da binciken da ake yi kan kutsen makiya  a cikin Hizbullah, Sheikh Naim ya yi shara da cewa kungiyar “tana ci gaba da bincikenta a kan wannan batu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted