Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa

A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa  Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben

A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa  Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye.

Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IEC) ta fitar dazu.

Duk da cewa sakamakon zaben bai ƙare ba tukuna, amma Ouatara da ke jagorantar tun 2011 yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na huɗu a kan karagar mulkin ƙasar, bayan sake zaɓensa a 2015 da 2020.

A wannan Litinin, Hukumar zaɓe ta ƙasa da ƙasa (IEC) ta sanar da cewa Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na gaban abokan hamayyarsa huɗu:

Simone Ehivet na Movement of Capable Generations (2.42%), Jean-Louis Billon na Democratic Congress (3.09%), Ahoua Don Mello mai zaman kansa (1.97%), da Henriette Lagou na ƙungiyar jam’iyyun siyasa don zaman lafiya (1.15%).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments