Hamas Ta Ce: Kungiyar Ta Ba Da ‘Yanci Ga Masu Shiga Tsakani Zabar Membobin Kwamitin Gudanar Da Gaza

Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza Khalil

Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza

Khalil al-Hayya, shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: ƙungiyar ta Hamas ta bai wa masu shiga tsakani ‘yancin zaɓar membobin kwamitin da za su gudanar da mulkin Gaza, wanda zai sami cikakken iko a yankin.

A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Al- Jazeera a yammacin Lahadi, al-Hayya ya jaddada cewa; Akwai batutuwan ƙasa waɗanda ba wai Hamas kaɗai ke da alhakinsu ba, amma alhakin dukkan ƙungiyoyin ƙasa ne. Ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da dama da ƙungiyoyi, ciki har da Fatah.

Ya ƙara da cewa abin da aka cimma da ƙungiyoyin Falasɗinu kusan iri ɗaya ne da abin da ta cimma da Fatah. Ya lura cewa sanarwar ƙungiyar, a cikin sashe na farko, ta tabbatar da kafa kwamitin gudanarwa da masu shiga tsakani ke neman kafawa don ɗaukar alhakin gudanar da mulkin Gaza. Ya lura cewa Hamas ta amince da jerin sunayen da Misirawa suka gabatar.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta bai wa Misirawa jerin sunayen mutane sama da 40 waɗanda ba su da alaƙa da siyasa, kimanin watanni huɗu da suka gabata, kuma ya nemi su zaɓi waɗanda suka ga sun dace. Ya ƙara da cewa za a sami rundunar ‘yan sanda ta farar hula wacce ke ƙarƙashin kwamitin gudanarwa a yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments