Catherine Connolly ta lashe zaben shugaban Ireland

An zabi Catherine Connolly a matsayin shugabar Ireland a wani gagarumin sauyi na siyasa a Ireland, wanda hakan ke a matsayin wani lokaci na tarihi

An zabi Catherine Connolly a matsayin shugabar Ireland a wani gagarumin sauyi na siyasa a Ireland, wanda hakan ke a matsayin wani lokaci na tarihi ga siyasar neman sauyi a Ireland.

Connolly, ‘yar majalisa mai shekaru 68 daga Galway, ta lashe sama da kashi 64% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban  Ireland, wanda ya ba masu nazarin siyasar yankin  mamaki matuka, ta yadda ta kayar da manyan jam’iyyun da fitattun ‘yan siyasa.

Lokacin da ta kaddamar da Takara  a watan Yuli, an yi wa Connolly kallon bakuwa a yunkurinta na neman shugabancin Ireland, ‘yar majalisar dokoki mai sassaucin ra’ayi da neman sauyi, ta samu goyon bayan kananan jam’iyyun adawa kamar Social Democrats, Labour, da People Before Profit.

Duk da hadin gwiwar da ke tsakaninta da jam’iyyu masu yawa masu ra’ayin neman sauyi, amma ba a yi zaton za ta iya lashe zaben ba.

Tsarin zaben Ireland yana bawa masu jefa kuri’a damar bayar da fifiko ga ‘yan takara bisa jam’iyyunsu, inda wasu masu kada kuri’a da dama suka yi watsi da ‘yan Takara na jam’iyyunsu nag ado kuma suka kada mata kuri’a.

Ana hasashen cewa bisa ga ra’ayinta na nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu, za ta taka gagarumar rawa wajen kare hakkokin Falastinawa a dukkanin matakai na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments