Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher

Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur  sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna  musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar

Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur  sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna  musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar birnin El Fasher a hannun Dakarun RSF, tare da bayyan hakan a matsayin farganda da kuma yakin kwakwalwa.

Sanarwar ta ce, “A halin yanzu ana fuskantar wani kamfen na kafofin watsa labarai na ƙarya da nufin tayar da hankali da kuma karya zukatan mayakan, idan aka yi la’akari da cewa kwace hedikwatar rundunar na nufin faduwar birnin baki daya.” Sanarwar ta jaddada cewa “El Fasher shi ne shinge kumakatangar karfe da ta hana makiya kaiwa ga mafarkinsu.

Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan da Rundunar RSF ta sanar da ikonta na hedkwatar sojojin sa kai a El Fasher, birni na ƙarshe da har yanzu ke ƙarƙashin ikon gwamnati a yankin Darfur na yammacin Sudan.

Masu fafutuka a Sudan sun ba da rahoton ci gaba da faɗa a cikin birnin, suna tabbatar da cewa Rundunar Sojojin Sudan ta dakile wani babban hari da Rundunar RSF da ta ƙaddamar daga sassa biyar. Faɗa ya ta’azzara ne a yankin gabashin birnin, inda Rundunar RSF ta sanar da kwace ginin bataliyar sojoji ta Shida.

Duk da haka, shaidu da majiyoyin manema labarai sun nuna cewa ginin da Rundunar RSF ta sanar da kamawa tsohon gini ne da babu komai a cikinsa. Bayani game da halin da ake ciki a El Fasher  na cin karo da juna. Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da rundunar sojojin Sudan ta fitar kan batun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments