Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa.
Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta.
Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata.
Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga Oktoba, ke murnar cika shekaru 80 Da Ranar Majalisar Dinkin Duniya.
A wani biki da aka yi don haka, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Jawabi A Tehran, Yana Mai Bayyana Cewa, Zaman Lafiya Da Tsaron Kasashen Duniya, Da Kuma Huldar abota, an bayyana su a matsayin manyan manufofin Majalisar Dinkin Duniya.
Esmail Baghai ya nuna rashin jin dadinsa game da cewa ka’idodin Majalisar Dinkin Duniya tun lokacin da aka kafa ta sun kasance karkashin “keta haddi, cin zarafi akai-akai da rudani da nuna fifiko.”
Kisan kare dangi a yankunan Falasdinawa da gwamnatin Isra’ila ta mamaye da hare-haren soji kan kasashe da dama, ayyukan ta’addanci, da mamaye kasashe masu ‘yanci, duk tare da “cikakkiyar goyon baya da hadin gwiwa” na Amurka da wasu gwamnatocin Turai.” Inji shi.