Qalibaf: Sakon Iran, Rasha da China ga MDD manuniya ce ta hadin gwiwa mai karfi

Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin

Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku.

Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita.

“A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida daya daga cikin muhimman nasarorin da aka samu a manufofin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci, wanda ya samo asali ne daga da tsayin daka na al’ummar kasar, da kuma jurewa matsin lamba da takunkumi na Rashin adalci,” in ji shi.

A cikin wasikarsu, Iran, Rasha, da China sun tabbatar da cewa ranar 18 ga Oktoba ita ce ranar da aka kawo karshen kuduri mai lamba 2231, don haka batun yarjejeniyar nukiliya ta Iran ya kawo karshe a hukumance.

Kawancen sun kuma yi Allah wadai da yunkurin Birtaniya, Jamus, da Faransa suka yi na dawo da dukkan takunkumin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wa Iran a baya a kan batun shirinta na nukiliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted