Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila

Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin

Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta ce an tsare Hamdi ne a filin jirgi sama na San Francisco.

A ranar Lahadi CAIR ta yi kira da sake shi kuma ta zargi Trump da tsare shi saboda sukar da yake yi wa Isra’ila.

Masu goyon baya da masu fafutukar kare hakkin jama’a sun ce tsare Hamdi wani lamari ne na ramuwar gayya ta siyasa ga masu sukar Isra’ila, wadanda ake hukunta su a kan iyaka kafin ma su sami damar yin magana.

Tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hari kan Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, akalla Falasdinawa 68,000 ne suka mutu yayin da wasu 170,000 suka jikkata, yawancinsu mata da yara.

Kwararru sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya kaiwa daruruwan dubbai da zarar an gano wadanda suka bata ko kuma aka binne a karkashin baraguzan ginin.

A baya bayan nan dai Trump ya tsaurara matakan shige da fice, ciki har da shirye-shiryen na kafofin sada zumunta, akan masu nuna goyan Falasdinawa da kuma dawa da hare-haren Isra’ila kan Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments