Sojojin Pakistan Sun Tarwatsa Tankokin Yaki 6 Na Afghanistan A Rikicin kan Iyaka

Rahotanni sun bayyana cewa rikici na kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan inda dakarun sojin kasar Pakistan suka sanar da cewa sun tarwatsa tankokin yakin kasar Afghanistan guda 6 kuma an samu mummunar asara a cikin dakarunta a arangama da aka yi a yankin Kurram. Bayan tsagaita wuta na dan wani lokaci fadan […]

Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ta Lallasa Benin Da ci 4-0 A Uyo

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta lallasa abokiyar karawarta Benin da ci 4 da nema a wasan zagaye na 10 na neman tikitin zuwa gasar Kofin Duniya da suka buga a filin wasa na Godswill Akpabio dake birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.  Nijeriya ta jefa kwallayenta uku ta hannun dan wasan gaban Galatasaray Victor […]

Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu […]

Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu

Shugaban kasar Indonusiya  Prabowo Subianto ya sanar da irin ci gaban da aka samu game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaza, kana ya sanar cewa Jakarta a shirye take ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya, domin nuna irin tsawon lokacin da kasar ta dauka tana nuna goyon bayanta ga alummar […]

Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi. Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata. Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a […]

Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar  Barazanar Makiya

Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar.  Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a […]

Hamas Ta Ce HKI Tana Cikas Neman Gawawwakin Yahudawa A Gaza

Wani babban jami’in kungiyar Hamas a gaza ya bayyana cewa HKI tana dakile kokarinda kungiyar take na nemo da kuma mayar da gawakin yahudawan Sahyoniya da suka halaka saboda barin wutan da sojojin ta suka  yi kan gaza, wanda ya kai ga mutuwar jami’ansu da suka bawa aikin kula da yahudawan. Don haka wannan ya […]

Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine

Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia […]