Rahotanni sun bayyana cewa rikici na kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan inda dakarun sojin kasar Pakistan suka sanar da cewa sun tarwatsa tankokin yakin kasar Afghanistan guda 6 kuma an samu mummunar asara a cikin dakarunta a arangama da aka yi a yankin Kurram.
Bayan tsagaita wuta na dan wani lokaci fadan ya sake rikicewa tsakanin dakarun sojin Pakistan da na mayakan Taliban, inda Islam abad ta zargi Kabul da bada mafaka ga kungiyoyin yan ta’adda dake kawo rashin zaman lafiya a yanki, arangamar da akayi a baya bayan nan ta nun irin tashin hankali da ake ciki a iyakokin kasashen biyu
Kakakin sojin kasar Pakistan ya bayyana cewa dakarun kungiyar Taliban sun kaddamar da hari kan iyakar kasar a yankin Kurram, sai dai ya fuskanci mayar da martani soji da ya dace, inda pakistan tayi ikirarin cewa tayi nasarar tarwatsa tankokin yaki guda 6 da kuma wuraren da sojojin ke taruwa da hakan ya jawo mummunan asarar rayuka,