Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da zarge-zarge marasa tushe da kuma da’awar rashin gaskiya da rashin kunya da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan Iran, wanda ya yi a ranar Litinin a zauren majalisar dokokin yahudawan sahayoniya a gaban masu aikata laifukan kisan kare dangi.
A cewar wani rahoto da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar a jiya Talata, sanarwar ta ce: Amurka a matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa samar da ayyukan ta’addanci a duniya, kuma mai goyon bayan gwamnatin sahayoniyya ‘yan ta’adda masu aikata muggan laifuka, ba ta da wata kima wajen zargin wasu.
Bayanin ya ci gaba da cewa: Al’ummar Iran a yayin da suke mika godiya ta musamman ga jarumin da ba a taba ganin irinsa ba na kasar Iran da ma na yankin, Shahidai Hajj Qassem Soleimani, wanda ya taka rawa mara misaltuwa wajen tunkarar ta’addancin kungiyar ISIS da Amurka ta kafa, ba za su taba yafe ko manta da wannan danyen aikin da Amurka ta aikata na kashe wannan mutumi da mukarrabansa ba.