Babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ya jaddada cewa: ‘Yantar da sauran fursunonin manufa ce da ba za ta fice daga muhimman abubuwan da suka aka sa a gaba ba
Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul- Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya tabbatar da cewa: Ba za a taba mantawa da manufar ‘yantar da sauran jajirtattun fursunonin Falasdinu daga gidajen yarin ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya ba saboda yana daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan gwagwarmaya suka sa a gaba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: Kwamandan al-Nakhalah ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin cewa: Tutocin gwagwarmaya suna ci gaba da wanzuwa a kasa kuma ba su fadi ba, kuma al’ummar Falasdinu sun kasance masu daraja da karamci da jajircewa wajen tsayin daka.
Ya ce: “Abin da aka cimma a yau, wajen ‘yantar da fursunonin gwagwarmayar al’ummar Falasdinu, da ba zai yiwu ba, in ba tare da na mijin juriya da jarumtaka na mayakan gwagwarmayar Falasdinu ba, da kuma hadin kan al’ummar Falasdinu a baya bayan nan.”