Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan.
Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026.
Daga karshe dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0. Masu zanga-zangar suna fadar cewa An tsada bude wuta ne a gaza amma ba zaman lafiya.