Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu na dindindin a kwamitin sulhu a matsayin dokar da ta sabama doka kuma ba za ta yi tasiri a shari’a ba.

Kasashen turai saboda matsin lambar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA don haka wadannan kasashe basu da hurumin da za su ce wani abu kan jarjejeniyar,  tun da saboda su ne da Amurka dukkan yarjejeniyar ta wargaje

Minista Araqchi ya bayyana cewa batun yankin falasdinu yana daga cikin muhimman lamari a duniya yace hakki ne na shari’a ga alummar falasdinu su ci gaba da fafutukar neman yancin kai, kuma ya tunatar da sauran gwamnatoci nauyin da ya rataya a wunyansu game da batun, yace iran tana goyon bayan duk wani mataki na dakatar da kisan kare dangi da ake yi wa alummar gaza da kuma bayar da agaji da sake gina yankin na falasdinu.

Daga karshe ya yi kakkausar suka ga gwamnatin yahudawan sahyuniya da kuma muhimmanci kawo karshen mamayar yanki da take yi, da kuma bukatar gurfanar da wadanda suka yi laifi daga yahudawan domin hukunta su

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments