Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta sanar da cewa, sake gina Gaza na bukatar dala biliyan 70, kuma a halin yanzu ana

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta sanar da cewa, sake gina Gaza na bukatar dala biliyan 70, kuma a halin yanzu ana bukatar dala biliyan 20 domin fara ayyuka a cikin shekaru masu zuwa.

UNDP ta yi tsokaci game da abin ta kira alamomi masu kyau game da samar da kudade don sake gina Gaza, kuma ta ambaci Amurka da kasashen Larabawa da Turai a cikin wadanda zasu taka rawa a wannan batu.

Rahoto ya bayyana cewa yawan baraguzan dake jibge ya kai tan miliyan 55.

Da yake amsa tambaya game da lokacin sake gina Gaza, wani jami’in UNDP ya ce, mai yiwuwa a cikin shekaru goma zuwa 20 a iya sake gina yankin.

A gefe guda kuma, UNDP ta sanar da cewa an gano akalla gawarwakin mutane uku a wani aikin kwashe baraguzan da aka fara a Gaza, kuma ana sa ran samun karin gawarwaki masu yawa a yayin gudanar da wanann aiki.

Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya tabbatar da cewa sojojin Haramtacciyar Kasar  Isra’ila sun jefa bama-bamai sama da ton 200,000 a yankin.

A bangaren barnar da hare-haren ta jawo ga gidajen jama’a, an kiyasta cewa akalla gidaje 500,000 ne ko dai suka rushe baki daya ko kuma suka samu lahani.

Baya ga haka kuma Isra’ila ta rusa masallatai 835, da majami’u uku na Mabiya addinin kirista, sai kuma makabartu 40, sun sace sama da gawarwaki 2,450 a makabartu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments