Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai

Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ‎ ya ce, Bugun kirjin da shugaban

Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai

Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ‎ ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi.

Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau.

Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000.

Shi dai shugaban kasar ta Columbia yana daga cikin na gaba-gaba wajen sukar lamirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila saboda yakin Gaza da kuma Amurka wacce take goya mata baya.

A lokacin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na karshen nan, shugaba Gustavo Petro ya shiga cikin masu Zanga-zanga a birnin Newyork domin nuna goyon bayan Gaza da kuma yin kira da a kawo karshen yaki. Haka nan kuma kasarsa ta yanke huldar diplomasiyya da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

A wani jawabinsa na bayan fagen taron na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira da a kafa rundunar kasa da kasa domin ‘yanto da Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments