Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a jiya a ganawarsa da kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran a ranar Litinin.
Khatami ya fadawa kwamitin yadda al-amura suke dangane da harkokin tsaron kasar da kuma al-amura da suka shafiu siyasa, tsaro da shirin sojojin kasar Iran dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya.
Khatami ya kara da cewa yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka dorawa kasar, makiya sun yi amfani da dukkan fanninin yakin da suka mallaka, wadanda suka hada fasahar zamani mafi inganci da siyasa da kafafen yada labarai, da lalata tsaron kasa, da kuma amfani da ayyukan leken asiri. Tare da wannan Janar Khatami y ace, mun fidda sabbin tsare-tsare da fuskantar makiya da barazanar da suke wa kasar. Wanda muna fatan wadannan sabbin makatan zasu ladabtar da mikaya su kuma dandana masu radadin wanda ya dace da su. Ya ce abinda ya tabbata a duniya a halin yanzu shi idan kana da karfi za’a iya yin koma, kuma mun gansu a fili a gaza, da nan Iran da Siriya , Qatar da kuma Lebanon. Ya ce mun dauki wadannan sabbin matakan ne dai da umurnin Jagoran juyin juya halin musulunci na cewa ‘Ku kasance masu karfi da Jajircewa’.