Wani babban jami’in kungiyar Hamas a gaza ya bayyana cewa HKI tana dakile kokarinda kungiyar take na nemo da kuma mayar da gawakin yahudawan Sahyoniya da suka halaka saboda barin wutan da sojojin ta suka yi kan gaza, wanda ya kai ga mutuwar jami’ansu da suka bawa aikin kula da yahudawan.
Don haka wannan ya sa suka rasa samun wadan nan jami’insu saboda sun mutu, sun kuma mutu tare da yahudawan da suke hannunsu. Kungiyar Hamas bata san a dai dai inda suke ba a lokacinda aka kashe su, don haka akwai bukatar lokaci kafin su gano wadannan mutane.
Wasunsu sun karkashin burmudhin gine-gine a gaza wanda yake bukatar kwacesu kafin a kai ga gawakinsu. Don haka lai gwamnatin yahudawanne da sojojinsu. Ya ce, kafin haka mun yi kashedi ga HKI kan cewa hare-harensu yana barazana ga ruyuwar wadan nan yahudawa.
Ya ce a halin yanzu sun mika yahudawa 20 da ransu da kuma gawaki 4. Amma a halin yanzu yahudawan suna barazanar zasu rufe kofar Rafah su kuma rage yawan agajin da ke shigowa Gaza. Daga karshe yace, duk tare da matsaloli Hamas tana kokarin ciki al-kawalin da suka dauka.