Zelensky : Ban Ga Laifin Da Na Yi Wa Trump, Ballantana In Nemi Afuwa

Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in […]
Hamas Ta Yi Watsi Da Shawarar Isra’ila Na Tsawaita Matakin Farko Na Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau […]
Al-Houthi : Isra’ila Na fakewa Da Goyan Bayan Amurka Tana Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza

Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: […]
Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila

Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza. “Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da […]
A Yau Ce Dokar Haramta Amfani Da Tankunan Mai Masu Daukar Lita 60,000 A Najeriya

A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory […]
Iran Ta Zama Zakara A Damben Gargajiya Ta 2025 UWW Wanda Aka Gudanar A Kasar Albaniya

Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a […]
Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu

Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin […]
Yemen Ta Ce A Shirye Take Ta Koma Yaki Idan Yaki Ya Sake Barkewa A Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga […]
Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi

Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, […]
An Yi Jana’izar Shahidan Hizbullah Fiye Da 100 A Kudancin Lebanon

A jiya Juma’a ne dai aka yi jana’izar shahidan Hizbullah 130 a garuruwan Aytas-sha’ab da Aytarun da suke da kudancin Lebanon. Tashar talabijin din al-manar ta watsa taron jana’izar shahidai 95 da su ka yi shahada watanni uku da su ka gabata a yayin yaki da HKI. A garin Aytrun da shi ma yake a […]
An Yi Musayar Yawu A Tsakanin Shugabannin Kasashen Amurka Da Ukiraniya A Fadar White House

Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky […]
Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka

Fira ministan hakar Habasha Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan […]
Rasha Za Ta Bunkasa Kai Wa Nahiyar Afirka Alkama

Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan […]