A jiya Juma’a ne dai aka yi jana’izar shahidan Hizbullah 130 a garuruwan Aytas-sha’ab da Aytarun da suke da kudancin Lebanon.
Tashar talabijin din al-manar ta watsa taron jana’izar shahidai 95 da su ka yi shahada watanni uku da su ka gabata a yayin yaki da HKI.
A garin Aytrun da shi ma yake a kudancin Lebanon an yi jana’izar shahidai 35.
Dukkkanin jana’izar biyu ta sami halartar dububan mutane daga cikin garuruwan da kuma wajensu.
A gefe daya, a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar mutanen a garin Aytatun, sojojin HKI sun kai hari a gefen garin, sai dai babu rahoto akan shahada ko jikkatar mutane.
Dan majalisa mai wakilntar Hizbullah a majalisar dokoki Hassan Fadlallah wanda kuma shi ne shugaban bangaren masu goyon bayan gwgawarmaya a majalisar, ya gabatar da jawabi a wurin jana’izar, inda ya bayyana cewa; Shahidan sun kwanta dama ne a fagen dagar kare daukakar al’ummar Lebanon.
A garin Aytas-sha’ab, an yi taho mu gama mai tsanani a tsakanin dakarun Hizbullah da sojojin mamayar HKI a lokacin yakin 2006, kuma a wannan yakin ma abinda ya faru kenan,’kamar yadda Fadlallah ya bayyana.
Dan majalisar ya kuma jaddada cewa; Za a sake gina wannan garin, kuma yin hakan nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Lebanon.