Iran Ta Zama Zakara A Damben Gargajiya Ta 2025 UWW Wanda Aka Gudanar A Kasar Albaniya

Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a

Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla.

Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a wannan wata a fagen kasa da kasa. Tawagar damben gargaji ta kasar Iran ita ce zakara a gasar damben na wannan shekara ta 2025 haka ita ce zakara a gasar shekara ta 2024.

An gudanar da gasar ne a ranakun 27-28 na watan Fabrayrun wannan shekara, wato 2025UWW, wanda ya jawo hankalin masu shaawar wasan a duniya.

Daga cikin yan wasan da suka sami lambar zinari sun hada har da  Ali Momini mai nauyin (57) Rahman Amouzad (65) Kamran Ghasempour da kuma Amir Hussain Zare.(125).

Sai kuma mai lambar  Azurfa, wato Erfan Alizadeh (97). Younes Emami (74kg) ya sami tagulla. Iran ta sami maki  97 sai kuma kasar Japan wacce ta zo na biyu da maki 93.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments