Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi

Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria,

Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya.

Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan.

A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan.

A nan  Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon watan Ramadana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments