Zelensky : Ban Ga Laifin Da Na Yi Wa Trump, Ballantana In Nemi Afuwa

Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana

Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa.

Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka.

A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in ji shi kamar yadda ya bayyana a hirarsa da Fox News.

Sai dai ya bayyana cewa musayar yawun ba ta dace ba, sannan ya kara da cewa dangantakar da ke tsakaninsa da Trump za ta gyaru.

Tunda farko dai an soke taron manema labarai da aka shirya yi a fadar White House a jiya Juma’a, inda shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky suka shirya rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adinai tsakanin Amurka da Ukraine, bayan wani sa-in-sa mai zafi tsakaninsu biyun a ofishin Trump wato Oval office a safiyar ranar.

Bayan musayar yawun da aka yi a ofishin, Trump ya wallafa wata sanarwa a dandalin sada zumunta na Truth, yana mai cewa, “Na yanke shawarar cewa Shugaba Zelensky bai shirya ma zaman lafiya idan da hannu Amurka a ciki ba. Ya ci mutuncin kasar Amurka a cikin Oval office mai daraja. Zai iya dawowa idan ya shirya ma zaman lafiya.”

A nasa bangaren, Zelensky ya wallafa a dandalin sada zumunta na X cewa, “Zaman lafiya mai dorewa Ukraine ke bukata, kuma muna aiki don samun hakan.”

Haka zalika, shugabar Majalisar Tarayyar Turai Roberta Metsola ta bayyana a dandalin sada zumunta na X cewa, “Za mu ci gaba da yin aiki tare da kai don samun zaman lafiya mai dorewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments