A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar.
Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar. Dokar dai zata shafi ayyukan mutanen, don wasu zasu rasa ayyukansu.
Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport.
Sai kuma kungiyar masu dakon man fetur a kasar sun bayyana cewa zasu yi asarar tankuna na kimani naira biliyon 300 saboda wannan haramcin.