Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila

Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da

Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza.

“Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da kayan aikin soji zuwa Isra’ila amfani da tashoshin jiragen ruwanmu; kamar yadda,” Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Firayim Ministan Malaysia Anwar Ibrahim da Shugaban Colombia Gustavo Petro suka rubuta a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mujallar harkokin waje ta buga a wannan makon.

Sun jaddada cewa yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya fallasa gazawar tsarin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen rashin hukunta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi.

Malesiya da Colombia na daga cikin kasashen da suka goyi bayan korafin kisan kiyashin da kasar Afrika ta kudu ta kai kan Isra’ila a kotun duniya ta ICJ.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments