An Yi Musayar Yawu A Tsakanin Shugabannin Kasashen Amurka Da Ukiraniya A Fadar White House

Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun

Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya.

Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru.

Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako.

Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa, yana son kunna wutar yakin duniya na uku,alhali bai taki komai ba.

Shi kuwa mataimakin shugaban kasar Amurka ya zargi Zylenisky da cewa , babu girmamawa ga Amurka da shugaban kasarta a cikin abinda yake yi..”

Shi kuwa shugaban kasar ta Ukiraniya ya ce, babu yadda za ayi , ya yi sasauci a gaban Putin na Rasha.”

Shugaban na Ukiraniya ya fice daga fadar White House ba tare da gabatar da taron manema labaru ba, kamar yadda tun da fari a ka tsara za a yi.

Bayan tafiyar tashi ne dai shugaban Amurka ya wallafa sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana cewa: Zylinesky ya wulakanta Amurka, amma zai iya dawowa idan ya shirya karbar zaman lafiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments